Home Home Katin Zabe: Kungiyar Alarammomi Ta Jihar Kaduna Ta Ja Hankulan ‘Ya’yan Ta

Katin Zabe: Kungiyar Alarammomi Ta Jihar Kaduna Ta Ja Hankulan ‘Ya’yan Ta

118
0
Shugaban kungiyar Alarammomi masu makarantun tsangayu ta jihar kaduna Gwani Sulaiman Idris Mai zube, ya yi kira ga daukakin Alarammomin Jihar su hanzarta yin rajistar katin zabe dana dan kasa.

Shugaban kungiyar Alarammomi masu makarantun tsangayu ta jihar kaduna Gwani Sulaiman Idris Mai zube, ya yi kira ga daukakin Alarammomin Jihar su hanzarta yin rajistar katin zabe dana dan kasa.

Gwani Sulaiman Idris ya bayyana haka ne a cikin wata sanarwa da ya raba wa manema labarai a Kaduna, inda ya bukaci wadanda ba su da katin zabe da na dan kasa su gaggauta yin hakan.

Malamin, ya kuma umurci daliban su da su ka kai shekaru 18 yin rajistar katin zaben su, lamarin da ya ce ya na da mahimmanci da tasiri a rayuwar su.

Sanarwar dai ta fito ne ta bakin jmai magana da yawun Kungiyar Alaramma Adamu Ahmad Nabara.