Home Labaru Shari’a: Dililin Da Ya Sa Na Ke Bijire Wa Umurnin Kotu –...

Shari’a: Dililin Da Ya Sa Na Ke Bijire Wa Umurnin Kotu – Malami

830
0
Abubakar Malami, Tsohon Ministan Shari'a Na Najeriya,
Abubakar Malami, Ministan Shari'a Na Najeriya,

Tsohon Ministan Shari’a kuma Atoni-Janar na kasa Abubakar Malami, ya ce ya kan saba wasu umurnin kotu da gangan a wasu lokuta saboda kare hakkin ‘yan Nijeriya.

Malami ya furta haka ne, yayin da ya ke amsa tambayar da Sanata Eyinnaya Abaribe ya yi ma shi yayin tantance shi a zauren majalisar dattawa.

Karanta Labaru Masu Alaka: Buhari Ya Na Farin Ciki A Kan Samun Nasarar – Malami

An dai tambayi Malami a kan dalilin da ya sa ya ki yin biyaya ga umurnin kotu na sakin wasu mutane kamar yadda kotu ta bada umurni.

Abubakar Malami, ya ce aikin sa ne kare hakkin duk ‘yan Nijeriya, kuma hakan ya fi muhimmanci a kan hakkin wani mutum daya tilo.

Tsohon Ministan ya kara da cewa, sassa na 36 da 37 da 39 na kundin tsarin mulki sun bukaci a mutunta hakkin kowane mutum, amma ya ce ‘yancin da mutane ke da shi ya na da iyaka.

Ya ce aikin shi ne kare hakkin kowane dan kasa, amma idan aka duba sashe na 174 na kundin tsarin mulki, duk lokacin da hakkin mutum daya ya ci karo da na ‘yan kasa baki daya, na ‘yan kasa ke yin galaba.

An Nada Shugabannin Kwamitoci a Majalisar Wakilan Najeriya