Home Labaru Gwamnatocin Tarayya Da Jihohi Sun Raba Naira Biliyan 762

Gwamnatocin Tarayya Da Jihohi Sun Raba Naira Biliyan 762

426
0
Hukumar Rarraba Arzikin Kasa, FAAC
Hukumar Rarraba Arzikin Kasa, FAAC

Gwamnatin tarayya da jahohi da kananan hukumomi sun raba naira biliyan 762 da miliyan 600 a tsakaninsu, daga cikin arzikin kasa da aka samu a watan Yuni kamar yadda rahotanni su ka bayyana.

Hukumar rarraba arzikin kasa FAAC ta sanar da haka, cikin wata sanarwa da ta fitar dauke da sa hannun babban akanta na kasa Ahmad Idris.

Sanarwar, ta ce Najeriya ta samu naira biliyan 652 miliyan 949 a watan Yunin da ya gabata, wanda ya kere na watan Mayu da kusan naira biliyan 81 da miliyan 218.

Karata Labaru Masu Alaka: FAAC Ta Raba Wa Gwamnatoci Naira Biliyan 679.69 Na Watan Mayu

Sai dai sanarwar ta ce, harajin kudin shigo da kaya da na fitar da su kasashen waje ya ragu matuka.

Kason kudaden dai, ya nuna gwamnatin tarayya ta samu naira biliyan 309 da miliyan 433, yayin da jahohi su ka samu naira biliyan 201 da miliyan 157, sai kuma kananan hukumomi da su ka samu naira biliyan 151 da miliyan 384, jahohi masu arzikin man fetur kuma sun samu naira biliyan 38 da miliyan 705.