Home Labaru Femi Gbajabiamila Ya Nada Shugabanin Kwamitoci 106

Femi Gbajabiamila Ya Nada Shugabanin Kwamitoci 106

313
0
Femi Gbajabiamila, Shugaban Majalisar Wakilai

Shugaban majalisar wakilai Femi Gbajabiamila, ya sanar da shugabanin Kwamitocin majalisar 106 da wasu guda uku na rikon kwarya.

A cikin sabbin kwamitocin kuwa akwai kwamitin kula da asusun jama’a wanda dan Majalisa Woleoke zai shugabanta.

Karanta Labaru Masu Alaka: Gbajabiamila Ya Nemi A Mika Kasafin 2020 A Satumba

Wasu daga cikin shugabannin kwamitocin sun hada da Muktar Aliyu Betara na kwamitin kasafin, yayin da Jimi Benson zai shugabanci kwamitin kula da bangaren tsaro, sai kuma Paschal Obi a matsayin shugaban kwamitin kula da cibiyoyin lafiya na kasa.

Sauran sun hada da kwamitin yaki da cin hanci da rashawa da zai kasance a karkashin shugabancin Nicholas Shehu, da kuma Abdulrazak Namdas a matsayin shugaban kwamitin kula da rundunar soji.

Nade-naden dai sun haifar da ka-ce-na-ce a tsakanin ‘yan majalisar, amma Dakta Abdullahi Balarabe Salame ya ce duk rabon adalcin da za a yi sai an samu masu korafi.