Home Labaru Buhari Ya Rantsar Da Muhammad Tanko A Matsayin Shugaban Alkalan Nijeriya

Buhari Ya Rantsar Da Muhammad Tanko A Matsayin Shugaban Alkalan Nijeriya

269
0
Buhari, ya rantsar da Tanko Muhammad a matsayin sabon Shugaban alkalan Nijeriya.
Buhari, ya rantsar da Tanko Muhammad a matsayin sabon Shugaban alkalan Nijeriya.

Shugaban kasa Muhammad Buhari, ya rantsar da mai shari’a Ibrahim Tanko Muhammad a matsayin sabon Shugaban alkalan Nijeriya.

Karanta Wannan: Tanko Mohammed Ya Zama Shugaban Alkalan Nijeriya

An dai gudanar da bikin rantsarwar ne a fadar Shugaban kasa da ke Abuja.

Ibrahim Tanko ya zama Shugaban alkalan Nijeriya na 18, inda ya karbi jagoranci daga hannun tsohon Shugaban alkalan Nijeriya Walter Onnoghen, bayan majalisar dattawa ta tantance shi a makon da ya gabata.

Wasu daga cikin mahalarta bikin rantsarwar kuwa sun hada da maataimakin Shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo, da shugaban majalisar wakilai Femi Gbajabiamila da mataimakin Shugaban majalisar dattawa Sanata Ovie Omo-agege.

Sauran sun hada da Shugaban ‘yan sandan Nijeriya, Mohammed Adamu, da gwamnan jihar Borno Babagana Zulum, da na ihar Bauchi, Bala Mohammed, da sakataren gwamnatin tarayya Boss Mustapha Shugaban ma’aikatan Shugaban kasa Abba Kyari.