Home Labaru Ganduje Sun Roki Kotu Kada Ta Karbi Shaidun Abba Kabir Yusuf

Ganduje Sun Roki Kotu Kada Ta Karbi Shaidun Abba Kabir Yusuf

1006
0

Gwamna Abdullahi Umar Ganduje da jam’iyyar APC, sun nemi Kotun Sauraren Kararrakin Zaben gwamnan Jihar Kano kada ta karbi tulin shaidun da Abba Kabir Yusuf na jam’iyyar PDP ya gabatar mata.

Abba Kabir Yusuf dai ya gabatar da shaidu 241 a gaban kotun, ya na kalubalantar nasarar Gwamna Abdullahi Ganduje na jam’iyyar APC.

Lauyan Abba da jam’iyyar PDP Adeboyega Awomolo, ya ce za su kara kai wasu shaidu domin kara inganta karfin tulin hujjojin da su ke da su.

Ya ce daga cikin kwafen shaidun da su ka gabatar wa kotu, har da ainihin takardar sakamakon zabe daga wasu mazabu a Kananan Hukumomin Albasu, da Bebeji, da Bichi, da Dambatta, da Garun Malam, da Gwarzo, da Karaye, da Kura, da Madobi, da Nasarawa, da Rano, da Rogo, da Sumaila, da Tudun Wada da kuma Warawa.

Sai dai lauyoyin Ganduje da hukumar zabe da jam’iyyar APC sun nuna rashin amincewa a gabatar da kwafen takardun sakamakon zaben na ainihi.