Home Labarai Sharaɗa Na Ƙalubalantar Zaɓen Gawuna A Kotu, Ya Ce Ba Abi Ka’ida A Zaɓen...

Sharaɗa Na Ƙalubalantar Zaɓen Gawuna A Kotu, Ya Ce Ba Abi Ka’ida A Zaɓen Fidda Gwani Ba

201
0

Ɗan majalisa mai wakiltar birnin Kano a majalisar wakilai Sha’aban Sharada, ya garzaya kotu domin ƙalubalantar zaɓen mataimakin gwamnan jihar Kano Nasir Gawuna a matsayin ɗan takarar gwamnan jihar na Jam’iyyar APC.

Sharaɗa ya bayyana wa kotun cewa an karya dokar zaɓe ta hanyar sanya wakilai masu zaben dan takara da doka ba ta ba su damar jefa kuri’a ba su jefa a lokacin zaben fidda gwani na ‘yan takarar kujerar gwamnan jihar Kano.

Dan majalisar, ya bukaci a soke zaɓen domin ba a bi ka’ida ba kamar yadda dokar zaɓe ta gindaya.

Babbar kotun tarayya inda a nan ne aka shigar da karar, ta ce za ta saurari ƙarar bayan an aika wa mataimakin gwamna Gawuna takardar sammaci.

Sai dai Lauyan Sharaɗa ya shaida wa kotun cewa ko da aka aika wa Gawuna takardar sammacin ya ki karba da gangan, yayin da Alkalin kotun mai shari’a M Liman ya dage ranar da za a fara sauraren karar zuwa kwanki 15 masu zuwa.

Leave a Reply