Home Labarai Naira Biliyan 187 Ba Za Ta Isa Aikin Kidaya A Najeriya Ba –...

Naira Biliyan 187 Ba Za Ta Isa Aikin Kidaya A Najeriya Ba – NPC

24
0

Hukumar Kidiya ta kasa ta sanar da cewa, Naira biliyan 187 da aka ware a kasafin kudi domin kirga al’umma da gidaje da aka shirya yi a watan Afrilu na shekara ta 2023 ta yi kadan.

Shugabar hukumar ta riko Ugoeze Mbagou ta sanar da haka, a wajen wani taron masu ruwa da tsaki da ya gudana a Abuja.

An dai tada batun sake kidaya a Nijeriya a karon farko, bayan shekaru 17 da aka yi irin sa a shekara ta 2006, wanda hakan ya saba da shawarar Majalisar Dinkin Duniya da ta shata tazarar shekaru 10.

Jaridu sun ambaro Mbagou ta na cewa, gudanar da kidaya a babbar kasa kamar Nijeriya ya na bukatar kudin da ya haura naira biliyan 187, don haka ta bukaci a sake duba kasafin kudin domin duba yiwuwar kara wani abu.

Sai dai ta ce rabin kudin kidayar za su fito ne daga kungiyoyin da ke bada tallafi ta wannan fannin ne.