Home Labaru Kiwon Lafiya Shan Inna: Za A Fara Yi Wa Yara Allurar Riga-Kafi A Jihar...

Shan Inna: Za A Fara Yi Wa Yara Allurar Riga-Kafi A Jihar Kwara

226
0

Gwamnatin jihar Kwara, ta ce ta kammala shirin fara aikin yi wa yara riga-kafin shan-inna a fadin jihar, kamar yadda wata Jami’a  a ma’aikatar Kiwon lafiyar ta jihar Abimbola Folorusho ta sanar a birnin Ilorin.

Kananan hukumomin da za a fara da su kuwa sun hada da Asa, da Baruten, da Ifelodun, da Ilorin ta kudu, da Ilorin ta yamma, da Ilorin ta gabas da kuma Moro, kuma za a fara aikin ne daga ranar 3 zuwa 23 ga watan Agusta.

Folorunsho ta ce, yin riga-kafin zai taimaka wajen sama wa yara kariya daga kamuwa da cutar, wanda shine babban dalilin maida hankali a kai da gwamnatin jihar ta yi, ta na mai bukatar iyaye su maida hankali sannan su mika ‘ya’yan su idan aka zo yi masu allurar.

Idan dai ba a manta ba, kungiyar kiwon lafiya ta duniya, ta bukaci kasashen duniya su maida hankali wajen kiyaye yin allurar riga-kafi a kasashen su.