Home Labaru Boko Haram: Ba Mu Da Wata Makabartar Binne Sojoji Ta Sirri –...

Boko Haram: Ba Mu Da Wata Makabartar Binne Sojoji Ta Sirri – Rundunar Soji

665
0

Rundunar sojin Nijeriya ta yi Alla-wadai da rahoton da jaridar ‘Wall Street Journal’ da ke kasar Amurka ta wallafa, wanda ke cewa rundunar ta binne a kalla sojojin ta 1000 a sirrance bayan mayakan Boko Haram sun kashe su a jihar Borno.

Sojoji Da aka Binne

Ta ce irin wanna rahoton ya na fitowa ne daga mutanen da ba su da masaniyar komai a kan atisayen rundunar soji da yadda ta ke gudanar da al’amuran ta, don haka ta ce ya zama dole ta fitar da jawabi domin sanar da jama’a al’adar rundunar ta girmama jaruman ta da aka kashe a filin daga.

Ta ce bisa tsarin rundunar sojin Nijeriya, su na girmama duk dakarun da su ka mutu a filin yaki, kuma su na bin duk matakan binne su bisa girmamawa kamar yadda ake yi a duk fadin duniya.