Home Labaru Albashi: Oshiomhole Ya Bukaci Ma’aikata Su Kalubalanci Shugabannin Siyasa

Albashi: Oshiomhole Ya Bukaci Ma’aikata Su Kalubalanci Shugabannin Siyasa

438
0
Oshiomhole Ya Jinjinawa Buhari Bisa Rage Kudin Man Fetur
Adams Oshiomhole, Shugaban Jam’iyyar APC Ta Kasa

Shugaban jam’iyyar APC na kasa Adams Oshiomhole, ya bukaci kungiyar kwadago ta kasa ta kalubalanci shugabannin siyasa don tabbatar da cewa an yi amfani da arzikin kasa wajen cika bukatun ma’aikata da sauran ‘yan Nijeriya.

Oshiomhole ya yi kiran a wajen wani taron karrama darakta janar na kungiyar kwadago ta duniya Guy Ryder da ya gudana a Abuja, inda ya nuna damuwa a kan halin ko-in-kula da shugabanni ke nunawa wajen inganta rayuwar ma’aikatan Nijeriya.

Yayin da ya ke jinjina wa shugaban kungiyar kwadago na duniya akan maida hankali da ya yi wajen daukar matasa aiki da nema wa jama’a hakkokin su, Oshiomhole ya ce ya kamata a maida hankali ga yawan mutane da rashin aikin yi ga matasa.

Ya ce ya kamata Nijeriya ta yi wani abu a kan hauhawar adadin mutanen ta, wanda ya ke karuwa da kaso uku duk shekara, sabanin tattalin arzikin ta da ke karuwa da kaso biyu duk shekara.