Home Labaru Kiwon Lafiya Shan-Inna: ERC Za Ta Tantance Najeriya Don Bata Shaidar Yin Sallama Da...

Shan-Inna: ERC Za Ta Tantance Najeriya Don Bata Shaidar Yin Sallama Da Cutar

467
0

Hukumar lafiya ta majalisar dikin duniya WHO ta ce Nijeriya za ta iya samun shaidar rabuwa da cutar shan inna kwata-kwata, idan ba a samu bullar cutar ba nan da shekara ta 2020.

Kodinatan shirin yi wa yara allurar rigakafi a karkashin hukumar Pascal Mkand ya ce hakan zai tabbata ne idan kwamitin majalisar a gamsu da ingancin kokarin kawar da cutar da gwamnatin Nijeriya ta ke yi, sannan ya ce kwamitin zai fara gudanar da bincike aka lamarin nan da mako mai zuwa.

Pascal ya bayyana haka ne a taron inganta hanyoyin kawar da cutar da kuma yi wa yara allurar rigakafi a Nahiyar Afrika da ya gudana a Abuja.

Sannan ya jinjinawa bangaran kiwon lafiya na Nijeriya bisa dakile yaduwar cutar, sannan ya yi kira ga gwamnatin Buhari ta mai da hankali wajen dakile yaduwar cutar shan-inna a Nijeriya.

Binciken da jami’an kiwon lafiya suka gudanar ya nuna cewa, wata sabuwar cutar shan inna mai suna Circulatin Vaccine ta bullo, sannan har ta fara yaduwa a kasashen Afrika guda 12.

Jami’an su ce mutum na iya kamuwa da wannan cuta ne idan akwai kwayoyin cutar shan inna a jikin sa.