Home Labaru Buhari Ya Nada Muhammad M. Nami A Matsayin Shugaban Hukumar FIRS

Buhari Ya Nada Muhammad M. Nami A Matsayin Shugaban Hukumar FIRS

346
0

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da nadin Muhammad M. Nami a matsayin shugaban hukumar tara kudaden shiga na kasa FIRS.

Rahotannin sun ce, Nami zai maye gurbin Tunde Fowler ne wanda wa’adin mulkin sa ya kare a ranar Litinin da ta gabata.

Muhammad M. Nami kwararre ne a bangaren harkokin haraji, kuma ya kammala karatun sa ne a jami’ar Ahmadu Bello da ke Zaria.

Mai magana da yawun shugaban kasa malam Garba Shehu ya fitar da wata takarda da ke cewa, Muhammad kwararre ne a bangaren haraji da kididdiga da kuma lissafi, sannan gogagge ne a sha’anin shugabanci.


Garba Shehu ya ce, Muhammad ya kuma mallaki lasisin aiki acibiyoyi daban-daban kuma ya yi a kalla cikin su har na tsawon shekaru 30, sannan ya yi aiki a cibiyoyin gwamnati da wanda ba na gwamnati ba, matakin da ya sa shugaban kasa Buhari ya aminta da hadin shi a matsayin shugaban hukumar tara vkudademn shina na kasa FIRS.