Home Labaru Sanata Danjuma Goje Ya Yi Murabus Daga Mukaminsa

Sanata Danjuma Goje Ya Yi Murabus Daga Mukaminsa

593
0
Danjuma Goje, Tsohon Gwamnan Jihar Gombe

Tsohon Gwamnan jihar Gombe Danjuma Goje ya ce, ya yi murabus daga neman mukamin siyasa domin ba masu tasowa damar nuna bajintar su.

Goje ya bayyana hakan ne a lokacin wani taro da wasu jiga-jigan  jam’iyyar APC su ka shirya ya kuma gudana a filin wasa na Pantami da ke jihar.

Tsohon gwamnan ya ce manufar yin hakan shine, ba wai ya bar harkokin siyasa ba ne, illar ya ja da baya domin ba wasu damar nuna kwarewa da nuna bajintar su.

Sanata Goje ya kara da cewa, akwai ‘yan siyasar da ke ganin ya dushashe musu tauraruwa, saboda haka ya ke ganin lokaci ya yi da zai ba wasu damar baje kulin su, wanda yanzu kofa a bude take ga duk mai bukatar neman wata kujerar jihar.

Sanatan ya cigaba da cewa, a matsayin sa na madubin dubawa a siyasar jihar, zai cigaba ba Gwamna Muhammad Inuwa Yahaya goyon baya domin ganin jihar ta cigaba.

A karshe sanata Goje ya yi alkawarin ba shugaban kasa Muhammadu Buhari da shugaban majalisar dattawa Ahmed Lawal da shugaban jam’iyyar APC na kasa Adams Oshiomhole goyon baya domin kaiwa ga nasara.