Akalla shaguna 41 ne suka kone bayan tashin wata gobara a Kasuwar Kurmi da ke Kano a ranar Litinin din nan.
Wannan kasuwa dai na daga cikin mafi dadewa kuma cibiyar kasuwancin Arewacin Najeriya.
Gobarar, wacce ta fara cid a misalin karfe Dayan a Asuba ta shafi shagunan da ke bangaren masu sayar da littattafai ne a kasuwar.
Kakakin Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kano, Saminu Abdullahi, yace sun samu rahoton gobarar ne daga wani mutum mai suna Malam Baba Nasidi.
Yace nan take suka aike da ’yan kwana-kwana wajen da misalin karfe 02:07 na asubahi, inda suka samu nasarar kashe wutar.
Kakakin ya kuma ce akalla shagunan wucin gadi 37 ne suka kone, sai kuma wasu manyan shaguna hudu da gobarar ta shafa sama-sama.
Ya ce tangardar wutar lantarki ce ta haifar da gobarar.
Daga karshe ya shawarci ’yan kasuwa da su tabbata suna kashe dukkan kayayyakin wutar lantarki kafin su bar shagunansu a kullum.