Home Labaru Gobara Ta Hallaka Mutane Da Dama A Tashar Jiragen Ruwa Na Fatakwal

Gobara Ta Hallaka Mutane Da Dama A Tashar Jiragen Ruwa Na Fatakwal

94
0

Gobara tayi sanadiyar konewar Jirage da kaya a babbar tashar jiragen ruwa ta Nembe-Bonny da ke birnin Fatakwal babban birnin Jihar Ribas.

Yanzu haka ana fargabar gobarar ta kuma yi sanadiyyar rasa rayukan mutane da dama, ciki har da wasu yara da ba a kai ga tantance adadinsu ba.

Ya zuwa yanzu dai ba a san musabbababin tashin gobarar ba, amma ana kyautata zaton wani jirgi dauke da mai ne ya fara kamawa da wuta kafin daga bisani wutar ta bazu zuwa wasu sassan tashar.

Sai dai wata majiyar tace masu dillancin kalanzir ta haramtacciyar hanya  ne suka yi musabbabin tashin gobarar.

Dama dai tashar ta Nembe-Bonny ta yi kaurin suna wajen harkalla da cinikin man fetur ba bisa ka’ida ba.

Anasa bangaren Kakakin Rundunar ’Yan Sandan jihar, SP Nnamdi Omoni bai yi Karin bayani kan lamarin ba.