Home Labaru Mutum 159 Sun Rasu A Abuja Cikin Shekarar 2021 – FRSC

Mutum 159 Sun Rasu A Abuja Cikin Shekarar 2021 – FRSC

42
0

Hukumar kiyaye haɗura ta kasa FRSC ta ce mutum 156 sun rasa rayukan su sakamakon hatsarin mota 850 da suka faru a yankin babban birnin tarayya Abuja a shekarar 2021.

Shugaban hukumar na Abuja Oga Ochi ne ya bayyana hakan yayin zantawa da manema labarai, inda yace akwai wasu Karin mutum 1,572 da suka ji rauni a hatsurran.

Ya kara da cewa Alƙalumman sun shafi daga watan Janairu zuwa watan Nuwamban nan da muke ciki.

Har ila yau ya kuma ɗora Alhakin yawan aukuwar hatsurran akan yawan saɓa dokokin tuƙi da mugun gudu da kuma rashin haƙuri daga masu tuka ababen hawa.