Home Labaru Seven Killed, Properties Destroyed As Suspected Bandits Block Major Road In Zamfara

Seven Killed, Properties Destroyed As Suspected Bandits Block Major Road In Zamfara

88
0

Ministan harkokin cikin gida na Najeriya ya ce kashi 74 na mazauna gidan yari a ƙasar na jiran shari’a ne.

Rauf Aregbesola wanda ma’aikatarsa ce ke kula da gidajen yarin ƙasar nan ya ce adadin mai yawa na samuwa ne sakamakon ƙaruwar ɓalle gidajen yari da ake yi a baya-bayan nan.

Ministan ya bayyana hakan ne yayin ƙaddamar da shirin aiwatar da shari’o’i ta intanet karon farko a Najeriya tare da taimakon hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta UNDP da kuma gwamnatin ƙasar Japan.

A cewarsa, fursuna 17,000 ne kaɗai daga cikin 68,000 aka yanke wa hukunci yayin da sauran ke jiran shari’a.

Har ial yau ministan ya alaƙanta hakan da tafiyar hawainiya da ake samu a tsarin shari’ar Najeriya.