Home Labaru ‘Yan Sanda Sun Kama ’Yan Bindigar Da Suka Kashe Hakimin ’Yantumaki

‘Yan Sanda Sun Kama ’Yan Bindigar Da Suka Kashe Hakimin ’Yantumaki

55
0

’Yan bindigar da suka kashe hakimin ’Yantumaki, Alhaji Abubakar Atiku Maidabino, sun shiga hannun hukuma.

Kakakin Rundunar ’Yan Sanda ta Jihar Katsina, SP Gambo Isa ya tabbatar da cafke bata garin.

Idan za a tuna, a watan Yulin shekarar 2021 ne ’yan bindiga suka je gidan hakimin suka kashe daya daga cikin masu gadin gidan, Gambo Isa kafin daga bisani suka kashe basaraken.

Daya daga cikin wadanda aka kama, wanda mazaunin garin Kagara da ke Karamar Hukumar Matazu ne, ya ce sun je garin tare da wasu da ake nema har yanzu, inda suka yi wannan aika-aikar.

Masarautar hakimin na karkashin Karamar Hukumar Danmusa na daya daga cikin kananan hukumomin da ke fama da ayyukan ta’addancin barayin daji a Jihar Katsina.