Home Labaru Makamashi: Minista Ya Kira Taron Gaugawa A Kan Matsalar Wutar Lantarki A...

Makamashi: Minista Ya Kira Taron Gaugawa A Kan Matsalar Wutar Lantarki A Nijeriya

66
0
Ministan harkokin lantarki Inijiniya Abubakar Aliyu, ya kira taron gaugawa na masu ruwa-da-tsaki domin lalubo mafita game da matsalar wutar lantarki da ta tsawwala a ‘yan kwanakin nan.

Ministan harkokin lantarki Inijiniya Abubakar Aliyu, ya kira taron gaugawa na masu ruwa-da-tsaki domin lalubo mafita game da matsalar wutar lantarki da ta tsawwala a ‘yan kwanakin nan.

Taron dai ya kunshi kamfanonin samar da wutar lantarki, da hukumomin gwamnati da masu zaman kan su da ke da ruwa da tsaki a harkar wutar lantarki da iskar gas.

An gudanar da taron ne a Abuja, inda Ministan ya ce gwamnati ba za ta amince da yadda lamarin wutar lantarki ya samu koma-baya ba, ya na mai cewa dole a samo mafita ga dukmatsalolin da ke janyo koma-baya ga yawan wutar lantarki da ‘yan Nijeriya ke samu a kullum.

Ministan, ya kuma gargadi hukumomi da kamfanonin harkar wutar lantarki su guji nuna wa juna yatsa, su maida hankali wajen tallafa wa juna domin tabbatar da ganin ‘yan Nijeriya su na samun isasshiyar wutar lantarki. Injiniya Abubakar D. Aliyu, ya ce gwamnati za ta cigaba da kokarin daukar matakai don ganin an samu karuwar wutar lantarkin da ake samarwa a Nijeriya.