Home Home Bincike: NBTE Ta Ce Akwai Matasa Miliyan 90 Marasa Aikin Yi A...

Bincike: NBTE Ta Ce Akwai Matasa Miliyan 90 Marasa Aikin Yi A Najeriya

66
0
Hukumar Kula da ilimin sana’o’i da kimiyya da fasaha a Najeriya NBTE tace akwai matasa kusan miliyan 90 da yanzu haka basu da ayyukan yi a Najeriya, cikin su harda wadanda suka kammala karatun digiri a jami’o’i.

Hukumar Kula da ilimin sana’o’i  da kimiyya da fasaha a Najeriya NBTE tace akwai matasa kusan miliyan 90 da yanzu haka basu da ayyukan yi a Najeriya, cikin su harda wadanda suka kammala karatun digiri a jami’o’i.

Shugaban hukumar, Farfesa Idris Muhammad Bugaje ya kuma ce daga cikin wannan adadi, akwai matasa miliyan 10 da basa zuwa makaranta baki daya, kuma akasarin su almajirai ne da ke yawon bara.

Bugaje, ya danganta matsalar tsaron da ta addabi Najeriya da rashin ayyukan yi wanda ya mamaye sassan kasa, yayin da ya bukaci gwamnati ta mayar da hankali wajen koyar da ilimin sana’o’i ga matasa domin dogaro da kai.

Shugaban hukumar ya ce akwai matasa da dama da suka kamala karatun jami’a kuma suke dauke da shaidar mallakar digiri amma kuma basu da aikin yi.

Bugaje ya bada misali da kasar Bangladesh wadda ke koya wa matasanta ilimin sana’o’i, abin da ke bada damar kai su kasar Saudi Arabia domin yin aikace-aikace a bangarori da dama, abin da ke taimaka wa kasar samun kudaden waje.

Shugaban hukumar ya bayyana damuwa a kan kungiyar matasan da ake samu a jihar Kano wadanda ke zargin cewar gwamnati ta yi watsi da su, saboda haka za su lalata kadarorin da ta mallaka a sasan jihar, inda ya bukaci daukar matakan gaggawa kafin kungiyar tasu ta yi karfi yadda zata zama wata babbar barazanar tsaro a kasa baki daya.