Home Labaru Kasuwanci Sauya Fasalin Naira – EFCC Ta Nemi Taimakon Bankuna Da ‘Yan Canji Don...

Sauya Fasalin Naira – EFCC Ta Nemi Taimakon Bankuna Da ‘Yan Canji Don Kama Masu Laifi

107
0

Hukumar yaki da cin hanci da rashawa EFCC, ta nemi Bankuna da masu sana’ar canjin kudi su ba ta hadin kai domin kama masu laifi a harkokin kudi yayin da ake shirin sauya fasalin kudin Nijeriya.

Shugaban hukumar EFCC, Abdulrasheed Bawa ya yi kiran, yayin wani taro da manyan jami’an Bankuna da masu kamfanonin canjin kudi a Lagos.

Abdulrasheed Bawa, ya nemi bangarorin biyu su taimaka wajen sanar da hukumar EFCC cikin gaugawa duk wani abu da su ka gani wanda ya shafi alamar almundahana ko zamba, musamman a wannan lokaci da Nijeriya za ta sake sauya fasalin wasu daga cikin manyan takardun kudin ta.

Bawa, ya kuma bukaci bankuna da masu canji su sanar da hukumar EFCC duk wasu bayanai masu amfani cikin gaugawa, game da ajiyar kudin da su ke zargin akwai alamar rashin gaskiya da kuma sauya wa kudi ma’ajiya daga wani asusu zuwa wani.

Leave a Reply