Home Labaru Ilimi ASUU Na Shirin Komawa Yajin Aiki

ASUU Na Shirin Komawa Yajin Aiki

30
0

Kungiyar malaman jami’o’i ta Nijeriya ASUU, ta na shirin sake komawa yajin aiki bayan ta zargi gwamnati da rashin cika alkawarin ta na biyan bukatun su.

A wata tattaunawa da mataimakin shugaban kungiyar Dr Chris Piwuna ya yi da manema labarai, ya ce kungiyar ta na shirin gudanar da taron gaugawa domin yanke shawara a kan matakin da za ta dauka a cikin kwanakin nan.

Malaman dai su na korafi a kan yadda su ka ce gwamnati ba ta biya su albashin watanni takwas da su ka yi su na yajin aiki ba.

Dr Chris Piwuna, ya ce babu ko daya daga cikin alkawurran da su ka yi da gwmnati ta cika, kuma ba a rubuta wasika cewa an kara masu albashi ba kamar yadda su ka bukata.