Home Ilimi Kaduna: El-Rufai Ya Kallafa Kudin Makaranta Ga Daliban Sakandaren Jihar

Kaduna: El-Rufai Ya Kallafa Kudin Makaranta Ga Daliban Sakandaren Jihar

38
0

Gwamnatin jihar Kaduna, ta dawo da tsarin karbar kudin makaranta daga daliban makarantun sakandare na jihar.

Kwamishinar ilimi ta jihar Kaduna Halima Lawal ta sanar da haka, a cikin wata wasika da ta aike wa shugabannin makarantun sakandare na jihar Kaduna.

Halima Lawal, ta ce sake dawo da tsarin karbar kudin makarantar an yi shi ne sakamakon rashin kayan aiki da jihar Kaduna ke fama da shi.

Ta ce kowane dalibi da ke matakin babbar makarantar sakandare zai rika biyan Naira dubu 2 a kowacce shekara.

Wannan dai ya na zuwa ne, bayan Gwamna El-Rufa’i na jihar Kaduna ya ayyana ilimi kyauta ga dukkan dalibai mata a makarantun sakandare mallakin gwamnatin jihar a shekara ta 2018.