Home Labaru Saudiyya Ta Yi Magana Kan Gwamnatin Taliban

Saudiyya Ta Yi Magana Kan Gwamnatin Taliban

117
0

Saudiyya ta ce, tana fatan gwamnatin riƙo a Afghanistan za ta taimaka wajen tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali, tare da kawo ƙarshen tashin hankali da tsattsauran ra’ayi.

Ministan harakokin wajen Saudiyya Yarima Faisal bin Farhan, ya bayyana haka yayinda yake jawabi a wajen wani taron ministoci a kan rikicin Afghanistan.

Yarima Faisal bin Farhan, ya kuma jaddada goyon bayan kasar na zaɓin mutanen Afghanistan kan makomar ƙasar su, da kuma tsira daga katsalandan na wasu ƙasashen waje.

Taliban dai, ta razana ƙasashen yammacin duniya game da yadda ta naɗa tsofaffin mayaƙanta masu tsaurin ra’ayi a manyan muƙamai a sabuwar gwamnatin da ta kafa, ciki har da waɗanda Amurka ke nema ruwa a jallo.

Ya ce, Saudiyya mai ƙarfin faɗa a ji a Gabas Ta Tsakiya na da matuƙar muhimmanci ga tasirin taimaka wa Afghanistan wajen magance ƙalubalen da ke gabanta.