Shugaban Kamfanin matatan mai na kasa NNPC Mele kolo Kyari ya ce a cikin watanni biyar da rabi da suka gabata nijeriya ta yi asarar naira biliyan 17 sakamakon satar mai.
Kolo Kyari ya bayyana haka ne a lokacin wani zama da kwamitin sashen man fetur na majalisar dattawa ya gudanar, tare da cewa asarar da aka yi wannan shekarar ba kai ta shekarun baya ba, domin a 2018 nijeriya ta yi asarar naira biliyan 297 yayin da a 2019 aka yi asarar naira biliyan 26.
Shugaban ya ce an samu raguwar asarar ne saboda inganta harkokin da jami’an tsaro da gwamnati ta yi tare da hadin kan wasu jami’an tsaro da mutanen gari da shugabannin su.
Mele kola kyari ya cigaba da cewa, yanzu gwamnatin ta yanke shawara maida hakkin lura da bututun mai a hannun jami’an tsaro, sabanin ‘yan kwagilan tsaro da aka saba ba a baya.