Home Labaru Kama Shugaban Matasan Arewa Zai Iya Janyo Tashin Hankali- Tofa

Kama Shugaban Matasan Arewa Zai Iya Janyo Tashin Hankali- Tofa

582
0
Kama Shugaban Matasan Arewa Zai Iya Janyo Tashin Hankali- Bashir Tofa
Kama Shugaban Matasan Arewa Zai Iya Janyo Tashin Hankali- Bashir Tofa

Tsohon dan takarar shugaban kasa Bashir Tofa ya ce kama shugaban gamayyar kungiyoyin Arewa Nastura Sharrif karan tsaye ne ga dimokradiyya.

Tofa ya bayyana haka ne a cikin wani jawabi da ya fitar, tare da cewa, kama matashin na nuna rashin son jin gaskiya, wanda hakan ya sa ya yi ga shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bada umurnin sakin matashin cikin gaggawa.

Tsohon dan takarar ya kara da cewa, idan ba a sakin matashin ba, akwai yuwuwar hakan ya tayar da sabon rikicin da kashe wutar sa zai yi matukar wuya.

‘Yan Nijeriya dai, na cikin bacin rai matuka, sakamakon matsalar tsaro da talauci da rashin aiki ga kuma annobar COVID-19, wanda duk sun karar da hakurin mutanan Nijeriya.

A karshe ya ce ya kamata shugaba Buhari ya yi hattara, ya kuma san ainihin abokan sa na gaskiya da makiyan sa, wadanda ke bata sunan sa a don ‘yan Nijerriya