Home Labaru Ilimi Satar Jarabawa: Dalilan Da Su Ka Janyo Korar Daliban 63 – BUK

Satar Jarabawa: Dalilan Da Su Ka Janyo Korar Daliban 63 – BUK

210
0

Jami’ar Bayero da ke Kano, ta ce shiga harkallar satar jarabawa daban-daban ce ta haifar da kokar dalibai 63 da hukumomin makarantar su ka yi.

Daraktar Shirya Jarabawa da Daukar Dalibai Amina Umar Abdullahi ta sanar da haka, tare da Karin bayanin cewa an kuma yi wa wasu dalibai Dafkal har na tsawon shekara daya.

Ta ce tsatstsauran hukuncin, ya biyo bayan shawarwarin da Kwamitin Hukumar Gudanarwa na Jami’ar ya kafa a kan satar jarabawa, ya kuma gabatar da bayanin sa a ranar Larabar, 28 Ga Agusta na shekara ta 2010. An dai kama daliban daga Tsangayoyin Jami’ar daban-daban, sanna akwai wasu 19 da aka rubuta wa takardar gargadi da jan-kunnen shiga taitayi.