Home Labaru Gwamnatin Zamfara Ta Sa A Yi Bincike Game Da Batun Sa Qur’ani...

Gwamnatin Zamfara Ta Sa A Yi Bincike Game Da Batun Sa Qur’ani A Najasa

298
0

Gwamnatin jihar Zamfara, ta kaddamar da bincike akan sha’anin da ke tattare da al’amarin tsintar wasu fallayen Qur’ani Mai girma cikin najasa a wata makarantar Firamare.

An dai gano shafukan Littafi mai tsarki ne a makarantar Firamare ta Shattima da ke garin Gusau, wanda ya yi sanadiyar rufe makarantar har sai baba-ta-gani, tare da dakatar da malaman makarantar bisa umurnin gwamnan jihar Bello Matawalle.

Gwamnan wanda yanzu haka ya ke halartar taron zuba jari na Afrika a kasar Amurka, ya umurci hukumar makarantar ta kafa kwamitin bincike a kan lamarin.

A cikin wata sanarwa da sakataren gwamnatin jihar Bala Maru ya fitar a Gusau, gwamnatin ta sanar da kafa kwamitin mutane 23 a karkashin jagorancin Farfesa Jafaru Makau, yayin da gwamnatin jihar ta yi alkawain bada kyautar naira miliyan 2 ga duk wanda ya kawo bayanai masu amfani a kan lamarin.