Home Labaru Bincike: Gwamnonin Nijeriya Sun Biya Aikin Hajji Da Kudaden Talakawa

Bincike: Gwamnonin Nijeriya Sun Biya Aikin Hajji Da Kudaden Talakawa

893
0

Wani binciken kwa-kwaf ya nuna cewa, gwamnatocin jihohin Nijeriya sun kashe biliyoyn kudi daga asusun talakawa domin daukar nauyin mahajjata zuwa Saudiya da masu ziyarar ibada zuwa birnin Kudus, duk da cewa har yanzu wasun su ba su biya albashin ma’aikata ba.

Wadanda aka dauki nauyin su zuwa Makkah da birnin Kudus dai sun hada da malamai da limaman coci da jami’an gwamnati da ’yan siyasa da sauran ‘yan’uwa da abokan arziki kamar yadda rahotanni su ka bayyana.

Bayanai na cewa, har yanzu wasu gwamnatocin sun gaza biyan hakkokin ma’aikatan su na albashi, duk kuwa da tallafin makudan kudaden da su ka karba daga gwamnatin tarayya.

Binciken ya kuma gano cewa, da dama daga cikin jihohin da su ka dauki nauyin mahajjatan, sun yi watsi da manyan muhimman ayyukan ci-gaban al’umma da ke bukatar kulawa ta musamman.

A wannan shekarar dai, kudin aikin hajjin mutum guda daga Nijeriya ya kai naira miliyan daya da rabi, yayin da na masu ziyarar ibada zuwa birnin Kudus ya kai kimanin Naira dubu 710.

Leave a Reply