Home Labarai Satar Dalibai: An Sace Yara Kusan 200 A Ƙauyen Kuriga Na Jihar...

Satar Dalibai: An Sace Yara Kusan 200 A Ƙauyen Kuriga Na Jihar Kaduna

175
0

An sace ɗaliban firamare da na sakandare kusan su 200 a makarantar su da ke ƙauyen Kuriga a karamar hukumar Chikun ta jihar Kaduna da safiyar yau Alhamis lokacin da ɗaliban ke taron assembly da misalin karfe takwas da rabi.

Wani babban jami’in gwamnatin jihar Kaduna ya tabbatar da  afkuwar lamarin amma ya ce ya zuwa yanzu babu cikakken bayani kan lamarin.

Wani da ya shaida faruwar lamarin ya ce da misalain ƙarfe 8:30 ne bayan an gama asambili ke nan sai ga shigowar ƴan fashin daga kowane ɓangare, suka zo suka yi wa makarantar ƙawanya suka kwashi ɗalibai na firamare da sakandare kusan 200 har da malami ɗaya na sakandare suka wuce da su, y ace kuma sun harbi yaro ɗaya wanda aka garzaya da shi asibitin da ke garin Birnin Gwari.

Ya ce yaran da lamarin ya shafa shekarun su sun kama ne daga takwas zuwa 15, kuma yanzun ana cikin wani hali na fargaba tun bayan sace daliban.

Leave a Reply