Home Labarai Shugabancin Afirka: Tsohon Shugaban Najeriya Ya Nemi Kyautata Mulki

Shugabancin Afirka: Tsohon Shugaban Najeriya Ya Nemi Kyautata Mulki

116
0

Tsohon Shugaban kasa Cif Olusegun Obasanjo ya bayyana bukatar kasashen Afirka su fito da tsarin dimukuradiyya irin na Afirka da ya dace da nahjiyar domin zama mafita daga kalubale na rashin ci gaba saboda yadda shugabanin ke gudanar da mulki.

Yace nahiyar Afirka da ta rungumi tsari na dimukurdiyya da ta aro ta yafa daga kasashen trurai, ya maye gurbi wanda suke da shi na sarakunan gargajiya da ma kawar da sojoji daga mulki.

Ya kara da cewa gazawar da ake gani ta mulkin dimukurdiyyar ko dai na shugaba mai cikakken ikon na Amurka ko kuma tsarin firaminsta na kasar Birtaniya, wannan ya sanya tsohon shugaban Najeriya bayyana cewa akwai bukatar Afrika ta fito da tsarin dimukuradiyyar da ya dace da ita.

Kiran da Cif Obasanjo ya yi da ya kara amon wannan batu da aka dade ana yi na kara tabbatar da buklatar ci gaba da amfani da tsain dimukurdiyyar domin shine ya bada damar samun gwamnati ta jama’a kuma domin jama’a.

Da alamun kasashen Afirka za su ci gaba da lalube a kokarin samar da tsarin dimukuradiyyar da zai dace da al’addu, da adini da ma yanayin zamantakewar alumamr su domin samar da mulki bisa kamanta adalci da shine zai sanya samun ci-gaba mai dorewa a nahiyar da ke fuskantar babban kalubale na koma baya, da talauci da rigingimu.

Leave a Reply