Home Labarai Kashe Limamin Garin Mada: ‘Yan Sintiri 10 Sun Shiga Hannu

Kashe Limamin Garin Mada: ‘Yan Sintiri 10 Sun Shiga Hannu

116
0

Gwamnatin Jihar Zamfara ta ce an kama akalla ‘yan banga 10 kan zargin kashe wani malami a Jihar.

A ranar Talata ne aka yi wa Sheikh Abubakar Hassan kisan gilla, inda ake zargin ‘yan banga da hannu a lamarin da ya faru a Karamar Hukumar Gusau.

Wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan Zamfara, Sulaiman Bala Idris, ya fitar, ta bayyana cewa wadanda ake zargin ’yan sintiri ne ba ‘yan-sa kai a Jihar da aka tura kwanan nan ba ne.

Gwamnatin ta ce sakamakon binciken farko da ‘yan sanda suka gudanar ya nuna cewa daya daga cikin wanda aka kama tsohon dalibin malamin ne da aka kasha kuma bayanin zai taimaka wa hukumomi su fahimci lamarin da kuma daukar matakan da suka dace.

A cewar gwamnati, za ta gabatar da sakamakon binciken da ‘yan sanda suka gudanar da zarar an kammala shi.

Ta kuma aike da sakon ta’aziyya ga iyalan malamin da jama’ar garin Mada.

Leave a Reply