Mai Alfarma Sarkin Musulmi Alhaji Muhammad Abubakar, ya tabbatar wa masu yi wa ƙasa hidima a Sokoto cewa ba za a yi amfani da dokokin Shari’ar Musulunci ga waɗanda ba Musulmai ba.
Sultan Sa’ad ya bayyana haka ne a fadar sa da ke Sokoto, lokacin da masu kula da harkokin ‘yan bautar kasa a karkashin jagorancin shugaban su su ka kai ma shi ziyarar ban-girma.
Sarkin Musulmi ya kuma tabbatar masu cewa, za su samu tsaro duk da cewa akwai kalubalen tsaro a kasa baki daya.
Ya ce ba za a dora mwa wadanda ba Musulmi ba hukuncin Shari’ar Musulunci, ya na mai jaddada cewa babu wanda za a tursasa wa shiga Musulunci ba da son ran sa ba.














































