Site icon Liberty TV/Radio Hausa – Labaru – Tashar 'Yanci!

Sarkin Musulmai Ya Gaya Wa Masu Hidimar Ƙasa Cewa Shari’ar Musulunci Musulmai Kawai Ta Shafa

Mai Alfarma Sarkin Musulmi Alhaji Muhammad Abubakar, ya tabbatar wa masu yi wa ƙasa hidima a Sokoto cewa ba za a yi amfani da dokokin Shari’ar Musulunci ga waɗanda ba Musulmai ba.

Sultan Sa’ad ya bayyana haka ne a fadar sa da ke Sokoto, lokacin da masu kula da harkokin ‘yan bautar kasa a karkashin jagorancin shugaban su su ka kai ma shi ziyarar ban-girma.

Sarkin Musulmi ya kuma tabbatar masu cewa, za su samu tsaro duk da cewa akwai kalubalen tsaro a kasa baki daya.

Ya ce ba za a dora mwa wadanda ba Musulmi ba hukuncin Shari’ar Musulunci, ya na mai jaddada cewa babu wanda za a tursasa wa shiga Musulunci ba da son ran sa ba.

Exit mobile version