Home Labarai Tsaro: Dole Sojoji Su Yi Bayani Kan Makudan Kudaden Da Muka Basu...

Tsaro: Dole Sojoji Su Yi Bayani Kan Makudan Kudaden Da Muka Basu – Osinbajo

62
0

Mataimakin Shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo, ya bukaci sojojin Nijeriya su yi wa al’umma bayani akan makudan kudaden da gwamnati ta ba su domin gudanar da ayyukan tsaro.

Osinbajo, ya ce ‘yan Nijeriya su na da hurumin sanin irin makudan kudaden da gwamnati ta ware domin tunkarar matsalolin tsaron da su ka addabi kasar nan, domin kore shakku dangane da yadda gwamnati ke fuskantar kalubalen tsaro.

Mataimakin shugaban kasar, ya ce abin takaici ne kowane lokaci idan an yi maganar tsaro, sai wasu sojojin rika cewa ba su da kayan aiki, don haka ya dace ma’aikatar tsaro ta gabatar da wani tsarin da zai rika bayyana irin kudaden da su ke kashewa a bangaren tsaro.

Osinbajo ya kara da cewa, ya dace a ce Nijeriya ta shawo kan matsalar ‘yan bindigar da ake fama da ita ta wajen nuna kwarewa da kuma nuna dabarun yaki.