Home Labaru Sarkin Daura Ya Gamsu Da Biyayyar Da Osinbajo Ke Yi Wa Buhari

Sarkin Daura Ya Gamsu Da Biyayyar Da Osinbajo Ke Yi Wa Buhari

458
0

Mai martaba Sarkin Daura Umar Farouk Umar, ya yaba da irin biyayyar da mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo ke yi wa shugaba Muhammadu Buhari.

Sarkin ya bayyana haka ne, yayin da ya ke bayani game da irin kyakkyawar alakar da ke tsakanin shugaba Muhammadu Buhari da mataimakin sa Yemi Osinbajo.

Mai martaba ya bayyana haka ne, a wajen bikin nadin sarautar Dan Madamin Daura da aka yi a karshen makon da ya gabata,  inda manyan kasa da dama su ka samu halarta.

Sarkin Daura, ya ce an jarraba mubaya’ar da Osinbajo ke yi wa shugaba Buhari, ya na mai cewa, irin wannan gaskiyar da jajircewa da kuma sadaukar da kai ake bukata domin Nijeriya ta cigaba.

Ya ce su na sane da halin da shugaba Buhari da mataimakin sa Osinbajo su ka samu Nijeriya, amma a yau abubuwa su na sauyawa sakamakon kokarin da su ke yi.