Gwamnan jihar Kaduna Nasiru El-Rufai, ya bada umarnin biyan kusan malaman firamare dubu 8 da 500 daga cikin dubu 39 da gwamnatin jihar ta dauka aiki basussukan da su ke bi a cikin makon nan.
A cikin wata sanarwa da mai ba gwamnan shawara na musamman a kan yada labarai Muyiwa Adekeye ya fitar, gwamnan ya nuna rashin jin dadin sa a kan yadda kananan hukumomi su ka rike wa malaman makarantar hakkokin su.
Hakan kuwa, ya faru ne da sabbin malaman makarantar firamare da aka dauka a rukuni na biyu a jihar Kaduna.
Ya ce bayan bayani daga ma’aikatar kanananan hukumomi da hukumar SUBEB, gwamnatin jihar ta gano cewa kananan hukumomi su na rike da kusan naira miliyan 1 da dubu 800 na albashin malaman makarantar da aka dauka a karo na biyu.
Gwamnan El-Rufa’i dais hi ne gwamna na farko da ya fara biyan ma’aikatan jihar sa sabon karin albashin da shugaba Buhari ya sanya wa hannu bayan samun sahalewar majalisun kasa.
You must log in to post a comment.