Home Labaru Karin Albashi: Ko Gwamnoni Su Biya Mu Ko Su Sauka Kawai –...

Karin Albashi: Ko Gwamnoni Su Biya Mu Ko Su Sauka Kawai – NLC

437
0
Kungiyar Kwadago Ta Nijeriya, NLC
Kungiyar Kwadago Ta Nijeriya, NLC

Kungiyar Kwadago ta Nijeriya NLC, ta ce ya zama wajibi Majalisun Dokoki na Jihohi su tilasta wa gwamnoni biyan karin albashi ga ma’aikatan kowace jiha.

Babban Sakataren kungiyar na Kasa Emmanuel Ugboaja ya yi wannan kira, yayin da ya ke tattaunawa da manema labarai a a Lagos, inda ya ce duk gwamnan da ya ki biyan karin albashin a gaggauta tsige shi kawai.

Sakataren ya cigaba da cewa, gwamnonin Nijeriya sun bayyana cewa ba za su iya biyan fiye da karfin kowace jiha ba, sai dai kuma kungiyar ta ce babu wani dalilin da zai sa gwamnonin su yi korafi a kan biyan mafi karancin albashi na naira 30,000.

Ya ce babban laifi ne ga Nijeriya idan har wani gwamna ya murje idon sa cewa ba zai iya biyan karin albashi ba, alhalin wasu daga cikin su shatar jirgin sama su ke dauka a duk inda za su je balaguro.

Leave a Reply