Home Labaru Sarautar Kano: Kotu Ta Haramata Nadin Sabbin Sarakunan Da Ganduje Ya Yi

Sarautar Kano: Kotu Ta Haramata Nadin Sabbin Sarakunan Da Ganduje Ya Yi

390
0

Wata babbar kotun jihar Kano, ta bayyana sabbin masarautu hudu da gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje ya kirkira a matsayin haramtattu.

Kotun dai ta bada umarnin rushe sarakunan, tare da komawa karkashin tsarin da ake har sai an kammala sauraren karar da aka shigar a kan nadin sabbin sarakunan.

Idan dai ba a manta ba, gwamna Ganduje ya nada sabbin sarakunan yanka hudu a jihar Kano, biyo bayan amincewa da dokar kirkirar sabbin masarautu da majalisar dokoki ta jihar Kano ta yi.Tun kwana daya kafin bikin nadin sabbin sarakunan, wata kotun jihar Kano ta bukaci Ganduje ya dakatar da gudanar da bikin nadin sabbin sarakan, amma sai gwamnatin jihar ta ce umarnin ya zo mata ne bayan ta riga ta ba sabbin sarakunan takardar nada su.

Leave a Reply