Home Labaru Samar Da Tsaro: Ba Mu Gaza Ba Wajen Yaki Da Masu Satar...

Samar Da Tsaro: Ba Mu Gaza Ba Wajen Yaki Da Masu Satar Mutane – Dambazau

284
0
Abdulrahman Dambazau, Ministan Harkokin Cikin Gida

Gwamnatin tarayya ta ce ana samun nasara a yaki da migayun ayyukan da ake aikatawa musamman satar mutane don neman kudin fansa.

Ministan harkokin cikin gida Abdulrahman Dambazau ya bayyana haka, a wajen taron shugabannin rundunonin ‘yan sanda na kasashen yammacin Afirka a Abuja.

Ya ce gwamnati na aiki tukuru da hadin-kan wasu shugabanni wajen ganin ta shawo kan matsalolin tsaro musamman garkuwa da mutane.

Manufar taron, wanda ya samu halartar jami’an ‘yan sanda na kasa da kasa ita ce, duba kalubalen tsaro da yankin ke fuskanta da kuma yadda masu aikata laifi ke ketara iyakokin kasashe.

Janar Dambazau ya ce, a baya ba a san matsalar satar mutane ba, amma a halin yanzu an dukufa ana tuntubar juna da wasu shugabanni daban-daban na yankuna don ganin an kawo saukin wannan lamari.