Home Labaru Sarauta: Sarkin Karaye Ya Daga Darajar Mahaifin Sanata Rabi’u Kwankwaso

Sarauta: Sarkin Karaye Ya Daga Darajar Mahaifin Sanata Rabi’u Kwankwaso

876
0
Mai martaba Sarkin Karaye Alhaji Ibrahim Abubakar II
Mai martaba Sarkin Karaye Alhaji Ibrahim Abubakar II

Mai martaba Sarkin Karaye Alhaji Ibrahim Abubakar II, ya sanar da daga darajar mahaifin tsohon gwamnan jihar Kano Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso Alhaji Musa Saleh Kwankwaso.

Jami’in yada labarai na masarautar Karaye Haruna Gunduwawa ya bayyana haka , acikin wata sanarwa da ya raba wa manema labarai a Kano.

Sanarwar, ta ce daga likkafar mai martaba Sarki Ibrahim Abubakar II ta tabbata ne saboda muhimmancin sa da kokarin da ya ke yi na kawo ci-gaba a masarautar.

Biyo bayan wannan nadin, Alhaji Musa Saleh Kwankwaso ya zama daya daga cikin manyan ‘yan fadan Sarki masu zaben Sarakunan masarautar Karaye.