Home Labaru Harin Filato: An Kama Shugabannin Miyetti Allah Zuwa Abuja

Harin Filato: An Kama Shugabannin Miyetti Allah Zuwa Abuja

268
0
Harin Filato: An Kama Shugabannin Miyetti Allah Zuwa Abuja
Harin Filato: An Kama Shugabannin Miyetti Allah Zuwa Abuja

Jami’an rundunar ‘yan sanda ta jihar Filato, sun yi awon gaba da shugabannin kabilar Fulani a kananan hukumomin Mangu da Bokkos da Barkin Ladi da Riyom, inda aka garzaya da su Abuja domin yi masu tambayoyi a kan rikicin da ya afku a Bokkos.

Wata majiya ta ce, an kama mutanen ne, bayan gwamnan jihar Filato Simon Lalong ya umurci kwamishanan ‘yan sanda na jihar Isaac Akinmoyede, ya kama dukkan Ardon garin da Fulani su ka kai farmaki.

An dai tafi da dukkan Ardon da aka damke tare da shugaban kungiyar Miyetti Allah zuwa helkwatar hukumar ‘yan sanda da ke Abuja.