Home Labaru Siyasar Imo: Duk Wanda Ya Sauya Sheka Ya Rasa Kujerar Sa A...

Siyasar Imo: Duk Wanda Ya Sauya Sheka Ya Rasa Kujerar Sa A Majalisa – PDP

389
0
Siyasar Imo: Duk Wanda Ya Sauya Sheka Ya Rasa Kujerar Sa A Majalisa - PDP
Siyasar Imo: Duk Wanda Ya Sauya Sheka Ya Rasa Kujerar Sa A Majalisa - PDP

Uwar jam’iyyar PDP ta kasa, ta ce duk wadanda su ka sauya sheka a majalisar dokoki ta jihar Imo zuwa jam’iyyar APC sun rasa kujerun su.

A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun jam’iyyar PDP Kola Ologbondiyan ya fitar, ya ce masu sauya shekar ba za su iya ci-gaba da rike kujerun su ba, tunda jama’a sun yarje masu ne a karkashin jam’iayyar PDP.

Jam’iyyar PDP ta bayyana abin da ‘yan majalisar su ka yi a matsayin rashin kishi, tare da cin amanar jama’ar mazabun su, wadanda su ka zabe su a karkashin jam’iyyar PDP.

Ya ce masu sauya shekar sun rasa kujerun su na zama ‘yan majalisar jihar Imo, domin sai ta karkashin inuwar jam’iyyar da jama’a suka zabe su ne za su iya ci-gaba da mulkin su.

Kola Ologbondiyan, ya ce ba su da wani zabi da ya wuce su umarci hukumar zabe ta hada wani sabon zabe domin maye gurbin ‘yan majalisar da su ka sauya sheka.