Home Labaru Sarakunan Zamfara Sun Kalubalanci Gwamnatin Najeriya

Sarakunan Zamfara Sun Kalubalanci Gwamnatin Najeriya

690
0

Majalisar Sarakunan Jihar Zamfara ta bukaci Ministan tsaro, Mansur Dan Ali, ya bayyana sunayen sarakunan da ya ce, suna hada baki da ‘yan bindiga wajen kaddamar da farmaki kan al’umma.
Majalisar ta bayyana haka ne a wata sanarwa mai dauke da sa hannun Sarkin Anka kuma shugaban Majalisar sarakunan jihar Zamfaran Attahiru Muhammad Ahmad, a yayinda Sarkin Bungudu, Hassan Attahiru, ya karanta sanarwar bayan wani taron gaggawa da suka gudanar a birnin Gusau.
A cikin makon nan ne, Ministan Tsaron ya bayyana cewa, sabbin bayanan sirri sun nuna cewa, wasu manyan sarakunan gargajiya na da hannu a kashe-kashen da ake fama da su a wasu yankuna na arewacin kasar da suka hada da Zamfara da Katsina da Sokoto.
Majalisar ta bayyana cewa, muddin Ministan ya gaza bayanna sunayen sarakunan da ke hada baki da ‘yan ta’addan, hakan na nufin wani yunkuri ne na bata sunan sarakunan.

Leave a Reply