Home Labaru Buhari Ya Kalubalanci Shugabannin Afirka Kan Yawaitar Makamai A Nijeriya

Buhari Ya Kalubalanci Shugabannin Afirka Kan Yawaitar Makamai A Nijeriya

313
0
Shugaba Muhammadu Buhari
Shugaba Muhammadu Buhari

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, ya bukaci shugabannin kasashen yankin Sahel da Sahara su ba Nijeriya hadin kai wajen ganin an dakile shigowar kananan makamai cikin kasashen su.
Shugaba Buhari, ya yi wannan kiran ne a gaban taron kasashen yankin Sahel da Sahara, na yini guda wanda ya gudana a N’Djamena na kasar Cadi, a Asabar dinnan.
Buhari, ya ce wannan kiran da ya yi ya zama wajibi, saboda yadda kananan makamai suke shigowa Najeriya ta kan iyakokin kasashen,
Ya ce makaman suna karewa ne a hannun tsageru da ‘yan fashi da makami, da kuma masu garkuwav da mutane.