Home Labaru Kauran Bauchi Ya Dauki Lauyoyi 65 Don Kare Nasarar Lashe Zaben Gwamna

Kauran Bauchi Ya Dauki Lauyoyi 65 Don Kare Nasarar Lashe Zaben Gwamna

567
0

Sabon zababben gwamnan jihar Bauchi, Sanata Bala Muhammad, ya ce, tuni ya hango nasara a karar da Gwamna mai ci, Barista Muhammad Abubakar da jam’iyyar APC suka shigar gaban kotun kararrakin zabe.
Bala Muhammad, ya bayyana hakan ne a yayin da yake ganawa da manema labarai a Asabar dinnan, bayan da ya dauki lauyoyi har guda 65, wanda biyar daga cikin su manyan lauyoyin Najeriya ne wato SAN don kare nasarar da ya samu a gaban kotun sauraron kararrakin zabe na jihar.
Ya ce har yanzu dai ba a kawo musu wata bukata ta kotu ba, don haka basu san mai ake tuhumar su a kai ba, muddin kuma aka kawo musu takarda za su amsa kiran kotu.

Leave a Reply