Shugaban hukumar shirya jarabawar shiga manyan makarantun gaba da sakandire JAMB, Farfesa Ishaq Oloyede, ya ce hukumar ta gano yadda aka yi cuwa-cuwar bada guraben karatu dubu 706 da 189.
Farfesa Ishaq Oloyede, ya ce cuwa-cuwar bada guraben karatun ta shafi jami’o’i da kwalejojin Ilimi da na fasaha da sauran su.
Oloyede ya bayyana haka ne, a wajen taron masu ruwa da tsaki da ya gudana a Abuja, inda ya ce irin wannan mummunar dabi’ar ta na bata martabar Nijeriya.
Ya ce cuwa-cuwar ta shafi dukkan sassa 6 na Nijeriya, kuma ya hada da manyan makarantun gaba da sakandare masu zaman kan su da na gwamnati.
Farfesa Ishaq Oloyede, ya ce Kimanin jami’o’i 114 ne su ka bada guraben karatu dubu 67 da 795 ba a kan ka’ida ba, yayin da kwalejoji 137 su ka bada gurabe dubu 489 da 918.
You must log in to post a comment.