Home Labaru Jega Ya Bukaci A Karkatar Da Kudin Da Aka Kwato Zuwa Fannin...

Jega Ya Bukaci A Karkatar Da Kudin Da Aka Kwato Zuwa Fannin Tsaro

1249
0
Farfesa Attahiru Jega, Tsohon Shugaban Hukumar Zabe Ta Kasa
Farfesa Attahiru Jega, Tsohon Shugaban Hukumar Zabe Ta Kasa

Tsohon shugaban hukumar zabe mai zaman kan ta ta kasa INEC, Farfesa Attahiru Jega, ya shawarci gwamnatin Tarayya ta yi amfani da kudaden da ta kwato wajen inganta harkar tsaro domin fidda al’ummar Nijeriya daga mawuyacin halin da su ke fuskanta.

Farfesa Jega ya bayyana haka ne, yayin da yak e gabatar da jawabi a wani taro da cibiyar Hudaibiyya ta shirya a kwalejin shari’a ta Aminu Kano, inda ya ce kowane dan Nijeriya ya na bukatar ingantacciyar rayuwa, kuma hakki ne akan gwamnati da ta tabbatar da hakan.

Ya ce bai kamata rashin da’a da miyagun dabi’un shugabanni ya sa Nijeriya cikin mawuyacin hali ba, “yayin da sauran kasashe ke kokarin kawar da irin wannan mummunar dabi’ar daga tsarin su, inda matukar shugaba ya gaza, hakki ne a kan al’umma su sauke shi daga ofis.

Jega ya kara da cewa, akwai bukatar gaugawa Gwamnati ta zo da matakan da za su magance rashin tsaro da rashin daidaituwa a fannoni daban-daban.

Leave a Reply