Daya daga cikin ‘yan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP
Sanata Anyim Pius Anyim, ya bukaci gwamnatin shugaba
Buhari ta farka domin daukar mataki a kan rashin tsaron da ke
barazanar ruguza Nijeriya.
Tsohon sakataren gwamnatin tarayya, Sanata Anyim ya ce ana
bukatar jajircewa da sadaukarwa ne wajen daukar matakan
dakile matsalar tsaro maimakon farfaganda da yin ‘Allah-Wadai
a kafafen yada labarai.
Ya ce matakai masu tsauri da ya kamata a dauka wajen warware
matsalar tsaro sun hada da matakan soji na bai-daya a wuraren
da kalubalen tsaron su ka fi kamari, da bunkasa ababen more
rayuwa a yankunan karkara, da kuma bullo da shirin afuwa ga
‘yan bindigar da su ka yi tuba ta gaskiya, da shirin sama wa
matasa ayyukan yi a fadin kasar nan.
Sanata Anyim, ya ce ko da ya ke lokaci ya na kure wa jam’iyyar
APC, amma duk da haka ta na iya yunkurawa wajen ganin cewa
sunan ta bai shiga tarihi a matsayin gwamnatin da ta gaza wajen
tafiyar da al’ammuran Nijeriya ba.
You must log in to post a comment.